Romans 14

Marasa Ƙarfi da Masu Ƙarfi

1Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba ta yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba. 2Bangaskiyar mutum ta yarda masa yǎ ci kome, amma wanda bangaskiyarsa ba ta yi ƙarfi ba, yakan ci kayan lambu ne kawai. 3Mutumin da yake cin kowane irin abinci, kada yǎ rena wanda ba ya cin, wanda kuma ba ya cin kowane irin abinci, kada yǎ ga laifin mutumin da yake ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi. 4Kai wane ne har da za ka ga laifin bawan wani? Ko bawan yǎ yi aiki mai kyau, ko yǎ kāsa, ai, wannan ruwan mai gidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.

5Wani yakan ɗauki wata rana da daraja fiye da sauran ranaku; wani kuma yana ganin dukan ranakun ɗaya ne. Ya kamata kowa yǎ kasance da tabbaci a cikin zuciyarsa. 6Wannan mai ɗaukan rana ɗaya da muhimmanci fiye da sauran, yana yin haka ne ga Ubangiji. Wannan mai cin nama, yana yin haka ne ga Ubangiji, gama yakan yi godiya ga Allah; wannan da ba ya ci kuwa, yana yin haka ne ga Ubangiji yana kuwa yin godiya ga Allah. 7Gama ba waninmu da yake rayuwa wa kansa kaɗai, kuma ba waninmu da kan mutu don kansa kaɗai. 8In muna rayuwa, muna rayuwa ne ga Ubangiji; in kuma muna mutuwa, muna mutuwa ne ga Ubangiji. Saboda haka, ko muna a raye ko muna a mace, mu na Ubangiji ne.

9Saboda wannan ne Kiristi ya mutu, ya kuma sāke rayuwa domin yǎ zama Ubangiji na matattu da na masu rai. 10Kai kuwa, don me kake ganin laifin ɗanʼuwanka? Ko kuma don me kake rena ɗanʼuwanka? Gama duk za mu tsaya a gaban kujerar shariʼar Allah. 11A rubuce yake cewa:

“ ‘Muddin ina raye,’ in ji Ubangiji,
‘kowace gwiwa za ta durƙusa a gabana;
kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’ ”
Ish 45.23

12Don haka kowannenmu zai ba da lissafin kansa ga Allah.

13Saboda haka bari mu daina ba wa juna laifi. A maimakon, sai kowa yǎ yi niyya ba zai sa dutsen tuntuɓe ko abin sa fāɗuwa a hanyar ɗanʼuwansa ba. 14A matsayina na mai bin Ubangiji Yesu na tabbata ƙwarai cewa babu abincin da yake marar tsabta don kansa. Amma in wani ya ɗauka wani abu marar tsabta ne, to, a gare shi marar tsabta ne. 15In kana ɓata wa ɗanʼuwanka zuciya saboda abincin da kake ci, ba halin ƙauna kake nunawa ba ke nan. Kada abincin da kake ci yǎ zama hanyar lalatar da ɗanʼuwanka wanda Kiristi ya mutu dominsa. 16Kada ka bar abin da ka ɗauka a matsayi kyakkyawa yǎ zama abin zargi ga waɗansu. 17Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki, 18duk kuwa wanda yake bauta wa Kiristi a haka yana faranta wa Allah rai ne, yardajje kuma ga mutane.

19Saboda haka sai mu yi iya ƙoƙari mu aikata abin da zai kawo salama da kuma ingantawa ga juna. 20Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yǎ ci abin da zai sa wani yǎ yi tuntuɓe. 21Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗanʼuwanka yǎ fāɗi.

22Bari duk raʼayin da kake da shi game da wannan shaʼani yǎ kasance tsakaninka da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa ba ta ba shi laifi game da abin da shi da kansa ya ɗauka cewa daidai ne ba. 23Amma wanda yake da shakka yakan jawo wa kansa hukunci ne in ya ci, domin yana ci ba bisa ga bangaskiya ba; kuma duk abin da bai zo daga bangaskiya ba zunubi ne.

Copyright information for HauSRK